Labarai

SHARI’AR ZAKZAKY: Kotun Kaduna Ta Sanya Ranar Komawa Sauraron Karar Bayan Dawowa Daga Yajin Aiki

Daga Bilya Hamza Dass
Ranar 30/03/2021 shi ne kotun Kaduna ta yi zaman ƙarshe kan sauraren shari’ar Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky. A zaman ƙarshen kotun ta saurari shedu daga ɓangaren Sojoji, shaida na ƙarshe shi ne Manjo Janar AK Ibrahim, inda ya bayyana cewa; a ranar 12/12/2015 yana Kaduna Sai GOC ya kira shi ya shaida masa cewa an tare wa Buratai hanya a Zariya, don haka ya umarce shi da tafi Zariya domin Ƴan Shi’a na taruwa. Don haka yaje ya yi binciken makamai da kuma kamo Shaikh Zakzaky.

Ya ce don haka ya tura Laftanar Kanar O. Poul zuwa Husainiya. Ya tura Laftanar Kanar Babayo Darur Rahma. Shi kuma ya nufi Gyallesu. Yace sun isa qarfe 10 na dare.

Mallam Ibrahim Musa, shi ne shugaban Dandalin yaɗa labarai na Harkar Musulunci da Shaikh Ibraheem Zakzaky, yake yiwa jagoranci, ya tabbatar da kotun ta sanya ranar komawa kotun a shafin shi na Facebook yace; “Bayan dawowar yajin aikin ma’aikatan kotun a Najeriya an sake sanya ranar 1/7/2021 domin cigaba da sauraron shari’ar Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Sojojin Najeriya, sun kashe ƴaƴan Shaikh Ibraheem Zakzaky guda uku a gaban shi tare da ɗaruruwan Almajiran shi, suka binne wasu da ransu, kamar yanda sakataren gwamnatin jihar Kaduna, ya tabbatar a gaban kwamitin bincike na JCI da jihar ta kafa domin bincike da gano abubuwan da suka faru a harin Sojojin na ranakun 12,13,14 a gidan Shaik Zakzaky, Darul Rahama, Husainiyya a Zariya. Ya tabbatar da cewa; anyi ramin bai-ɗaya ga mutane 347 a garin Manɗo aka binne su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: