Sharhin Fim Din ‘Dr. Halima’


0 514

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Suna: Dr. HALIMA.

Tsara labari: Yakubu M. Kumo. Kamfani: Mai Kwai Mobies.

Daukar Nauyi: A. S Mai Kwai. Shiryawa: Abdul-Aziz Dan Small.

Bada Umarni: Abubakar A. S. Mai Kwai.

SHARHI: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Ali Nuhu, Aminu Shariff, Baballe Hayatu, Isa Bello Jah, Hajara Usman, Maryam Isa, Hafsat Idris, da sauransu.

Labarin Fim din Dr Halima, labari ne na wata mata ‘yar boko wadda ta kai har matakin digirin digirgir a fannin karatun boko, mai suna Dr. Halima (Maryam Isa). Bugu da kari, Dr.Halima mace ce mai son gayu da ado da kwalliya. Amma kuma Allah ya bata miji wanda babu ruwan shi da yaba wannan wankan da kwalliyar tata, wanda hakan yake matukar musguna mata, domin kuwa akwai wasu daga cikin abokan aikinta kullum basu da aiki sai yaba kwalliyarta da irin adon da take yi idan za ta zo aiki.

Fim din ya fara ne a inda aka hasko Dr. Halima a cikin mota ta karaso gurin aiki, inda ta fito da mayafinta a wuya tana taku dai-dai tana kasaita. Karasowar ta bakin kofar kamfanin nasu ke da wuya sai ga Manajan kamfani (Isah Bello Jah) da abokin aikinta Dass (Aminu Shariff) suma sun fito, ai kuwa nan take Dass ya rikice da kallon Dr. Halima yana kallon ta har da waiwaye yana murmushi har takai yana taka manaja a kafa amma shi bai ma son yana yi ba saboda hankalinsa gaba daya ya tafi kan Dr.Halima.

Bai dawo cikin hankalinsa ba har sai da manaja ya gaji da take shi din da ya yi, sai ya ture shi gefe sannan ya dawo cikin hankalinsa. A haka dai ake rayuwa a wannan kamfanin, yayin da Dass kullum sai ya shigo ofishin Dr. Halima yana ta kallonta yana yabon ta duk da cewa matar aure ce. Haka kullum yake laben lekenta idan ta shigo kamfani ko idan za ta fita. A haka dai ya rinka bibiyarta wanda har sai da ya cinma mummunan burinsa a kanta, bayan ya saka sunanta a matsayin wadda za ta wakilci kamfanin a taron Injiniyoyi da za a yi a garin Lagos.

Wanda a nan ya yi amfani da wannan dama ya aikata lalata da ita duk da kuwa dukanninsu masu aure ne. A daya bangaren Dr. Halima tana da miji mai suna Yusuf (Ali Nuhu) wanda ko kadan baya son yaba duk wani kyawunata da kuma kwalliyarta. Rikici ya fara a tsakaninsu ne a lokacin da ta dawo gida daga aiki ta same shi yana kwance a falo take bashi labarin cewa ai tana gasawa ‘yan ofis dinsu aya a hannu saboda tsabar wanka da kwalliya, take fada masa wai yau sabo da kallona da Manaja da Dass suke har zubar da takardun hannuwansu suka yi basu sani ba sabo da kallonta.

Tana cikin bashi labarin ne kuwa, take ya daka mata tsawa yana cewa ke saboda baki da hankali a matsayinki na matar aure shi ne har za ki iya kallona ina mijinki kina fada, min wai maza suna rikicewa idan sun ganki shasha kawai. Sai take ce masa to mene ne abun aibu naga ai kawai kyauna suka yaba. Kuma kai a matsayinka na mijina yau wajen watanmu hudu da yin aure amma baka taba yaban kwaliyata ba ko sau daya, haka dai suka watse cikin fushi. A haka dai Yusuf ya dauki fushi da Dr. Halima sakamakon halayyarta na rashin kamun-kai da rashin daraja aure da take nunawa kullum.

Har ta kai ya kaurace mata har na wasu lokuta baya kwana a dakinta. A nata bangaren Dr. Halima tana da kawa Zulaiha (Hafsat Idris) wadda take tattauna duk wani sirrinta da ita. Ta je tana neman shawararta a kan kaurace mata da mijinta ya yi na tsahon lokaci yayin da take fada mata cewa ko kadan kar ta sake ta bashi hakuri, ta bar shi da kansa zai kawo kansa. Shi kuma a nashi bangaren Yusuf yana da aboki (Baballe Hayatu) wanda kulluym yake bashi shawarar neman daidaito da matarsa, yana fada masa cewa wannan rikicin nasu ba zai haifa musu da-mai-ido ba.

Duk da cewa daga Yusuf din har Dr. Halima ba wanda yake jin dadin irin rayuwar da su ke, amma kowa ya kasa neman sulhu saboda jin girma da isa. Wanda sai daga baya ne sannan suka rusunawa juna suka daidaita tsakaninsu. Sai dai duk da daidaito da aka samu, Dr Halima ta kasa samun sukuni saboda kullum tunanin abinda suka aikata da Dass a Legas take yi. A kullum tana cikin takaici da kuma nadamar abunda ta aikata, duk da cewa ta kasa fadawa Yusuf ainihin abinda yake faruwa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 327

- Advertisement -

A karshe Dr Halima ta chanja dabi’arta ta zuwa gurun aiki da banzar shiga, inda ta koma yin shiga ta mutunci da kuma kama kanta a kodayashe. Shi kuwa Dass an kore shi daga aiki sakamakon wasu kudade da ake zargin ya bi ta kansu. Abubuwan Yabawa 1. Sunan fim din ya dace da labarin.

2. Hotuna sun dauku sosai, haka sautin ma ya fita sosai.

3. Akwai kalamai masu dadi a cikin shirin.

4.Nadamar da Dr. Halima ta yi a karshe.

5. Mummunan sakamako da Dass ya samu, saboda keta haddin Allah da ya yi.

6. Labarin mikakken labari ne domin kuwa ya samu nasarar rike mai kallo har karshe. Kurakurai

1. An samu hargitsewar sauti a fitowa ta farko na tsahon dakika 32 a cikin maganganun manaja da Dass inda aka ringa samun maimaituwar wasu kalmomi.

2. Kin yaba kwalliyar Dr.Halima da Yusuf mijinta yake yi bai kamata a ce ya zamar mata silar yin shigar banza idan za ta je aiki ba.

3. Kin bayyana Dr. Halima a gurun taron da taje yi a Lagos, zai saka wa mai kallo kokonto cewa an ya kuwa taron ta je, domin an hasko ta ne kawai a otel inda a nan ne suka yi abinda suka yi da Dass.

4. Sunan da ake kiran Aminu Sharif da shi wato “Dass” bai da ma’ana a addinance kuma bai dace da sunayen Hausawa ba.

5. A lokacin da Dr. Halima ta kirawo Zulaihat cikin dare da niyar fada mata za ta zo gidanta gobe, tana daga wayar sai kuma aka jiyo muryar Yusuf yana cewa “hello Halima”alhalin kuma ita zulaiha ta kirawo ba Yusuf ba, sai daga baya ne sannan aka ji muryar Zulaihat din ta fito.

6. Kin fadawa Yusuf cin amanar da Dr. Halima ta yi masa kuskure ne,ya kamata ta sanar da shi domin samun yafiyarsa ko akasin hakan.

7. A fitowa ta karshe da aka nuna Dr. Halima tana tuki har zulaiha ta kirawo wayarta, kafun a kirawo wayar an jiyo sautin murya na cewa “Action” sai kuma a ka yi shiru. To abun tambaya a nan shi ne, shin wannan fitowa ta karshe bata cikin ainihin fim din ne ko kuwa tana ciki? Idan har tana ciki to jin furucin “Action” kuskure ne, idan kuma bata ciki to ya kamata a nuna wani abu da mai kallo zai gane cewa ita wannan fitowar bata cikin fim din, wanda kuma ba a yi hakan ba. Karkarewa Fim din Dr. Halima fim ne mai labari mai matukar muhimmanci.

Domin ya bayyana irin yadda wasu matan suke kasa rike mutuncin aurensu idan suna zuwa aiki, wanda hakan ne yake tilastawa wasu mazan haramtawa matansu zuwa aiki. Sannan labarin ya nuna irin sakamakon da matan da suka kasa kama kansu suke samu, duba da irin abinda ya faru da Dr. Halima. Fim din ya samu aiki mai kyau domin kuwa ba a samu matsaloli da yawa a cikin aikinsa ba

 

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.