Sharhin Fina Finai

Sharhi Kan Shirin Dadin Kowa Sabon Salo Episode 83

Daga Gen. Sunusi

A shirinku na yau kunyi kokari wajen wanke KAWU MALA daga satar da yayi kun nuna yayi nadama har yakai kansa ga shugaban ma’aikatarsu don a hukuntashi a karshe dai bai rasa aikinsa ba saidai zai biya kudin Transformer din acikin Albashinsa…

Mun jinjina muku sosai duk da munso ace duk abinda ya faru mafarkine MALA yakeyi ba’a gaske ba.

Saidai kusani mutane zasu dade basu manta da abinda MALA ya aikata ba domin hakan ya sosa ran Mutane sosai! Ni kaina duk da na dauki film entertainment amma wannan abin yaki fita daga raina.

A shirye shiryenku na gaba yakamata ku dan rage hasko office dinsu MALA domin mutane zasuyi saurin mantawa da abinda ya faru a Episode na 81.

Sannan muna zuba ido muga makomar sauran abokan aikin MALA domin fa suna yi masa kallon barawo..

A karshe Muna kira ga duk wadanda suka ce sundaina kallon shirin DADIN KOWA kuyi hakuri an gyara matsalar..

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement