Kannywood

Shahararrun yan Fim sun jaddada goyon bayansu ga ƙungiyar matasan Arewa

Wasu daga cikin jaruman finafinan Kannywood sun ayyana goyon bayansu ga gamayyar kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Wasu daga cikin jaruman da suka jaddada goyon bayan nasu sun hada da Rabiu Rikadawa, Aisha Tsamiya, Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Adam Zango, Halima Atete da sauransu.

 

Idan ba’a manta ba dai, ita wannan kungiyar gamayyar matasan Arewa itace kungiyar nan data baiwa ya kabilar Ibo wa’adin tattara kayanka, inda suka bukaci dasu kwashe inasu inasu su koma yankin sun a kudu maso arewa.

Matasan sun bada wannan wa’adi ne sakamakon irin kalaman cin kashi da kungiyoyin fafutukar kafa kasar Biyafara ke yi ma yankin Arewacin kasar nan tun fil azal, inda suka yi barazanar raba Najeriya.

A wani labarin kuma, NAIJ.com ta ruwaito shuwagabannin kungiyoyin matasan sun gana da dattawan arewa tare da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a wani yunkurin shawo kan wa’adin da suka baiwa inyamurai.

Ga sauran hotunan kamar haka:

Aisha Aliyu Tsamiya

Jamila nagudu

Halima atete

 

Da sauransu

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.