-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Shahararren Dan Fim Hausa Karkuzu Nabodara Yana Cikin Mawuyacin Hali


1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zaune a karkashin barandar wani masallaci da ke Layin Zana a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato na samu Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da “Karkuzu Dan Kurmuzuzu Jikan Kozo Na Bodara Ikon Allah Wanda Sai Ta Allah Ta Yi.”

Karkuzu kamar yadda aka fi saninsa a harkar fina-fina Hausa ta Kannywod, ya shafe fiye da shekara 31 a harkar fim.

Na samu Karkuzu zaune ya yi tagumi duk da cewa a gefensa akwai wadansu dattawa uku da ke hira har da kyakyatawa, shi kuma bai ma san dawan garin ba, sakamakon nausawa da ya yi a cikin nauyayyen tunani, domin har na yi sallama dattawan suka amsa, bai san halin da ake ciki ba.

Na tsugunna na gaishe su, suka amsa cikin fara’a, sannan suka ci gaba da kallona dauke da zumudin son sanin abin da ke tafe da ni, a lokacin da na matsa kusa da Karkuzu ne, sai na ce musu na zo wurin Baba Karkuzu ne, inda daga nan sai suka ci gaba da labarinsu ba tare da sun kara saurara ta ba, tun da mun rika mun gaisa da su tun a farko.

Na matsa da bakina kusa da kunnen Karkuzu na dama, sannan na gabatar da kaina a matsayin dan jarida cikin sigar rada, fahimtar ko ni wane ne ya sanya ya ce, mu koma gefe don ya ji hakikanin abin da ke tafe da ni.

Muka koma gefe, inda ya zauna a kan wata kujera, ni kuma na tsugunna, sannan muka fara hira, inda ya ce, tabbas ba shi da gidan kansa, kuma yana bukatar a taimake shi a saya masa gida.

Ya ce, “Tabbas maganar ina zaune a gidan haya haka maganar take, amma gaskiyar yadda al’amuran suka faru har aka tura wannan sako a kafafen sadarwa na intanet an yi  kuskure wajen tura sakon.

Karkuzu mai kimanin shekara 83 ya bayyana cewa ya yi kira a wurin jama’a don su taimake shi su saya masa gida, sannan wadansu mutane ma sun yada a duniya cewa a taimake shi kasancewar ba shi da daki ko daya a matsayin mallakinsa.

Karkuzu wanda yake da mata daya da ’ya’ya bakwai ya ce rashin sanin tabbas ne ta sanya ya ce a sanar wa duniya halin da yake ciki.

Ya ce, “Ni Karkuzu din nan Wallahi Tallahi ba ni da daki ko guda daya a duniyar nan da sunan wannan nawa ne, sai na duba na ga tafiya tana tafiya, girma ya kama ni, gani da ’ya’ya, kuma gidan hayar da nake ciki an fitar da ni daga ciki, ko kuma in ce an ce za a sayar don haka in fita daga ciki.

“Dole ta sa na koma wani gidan hayar, hakan ne ya sa na roki wadanda suke watsa al’amuran duniya cewa su sanar wa duniya halin da nake ciki. Ina bukatar taimako, su taimake ni kamar yadda Allah Ya taimake su, su saya mini gida mai dakuna biyar ko shida, domin in karasa tsufana a ciki,” injishi.

Karkuzu a lokacin da idanunsa suka cika da hawaye ya ce yana so ya mallaki gida ne domin idan ya mutu ’ya’yansa su ce ga gadon da ya bar musu, “wannan shi ne dalilin da ya sa na ce a watsa a kafar sadarwa ta Facebook don a taimake ni, ko a tara kudi a saya mini gida, ko a samu wanda zai taimake ni ya saya mini gida.”

Karkuzu wanda ya fito a fina-finai fiye da 100 ciki har da ‘Macijiya’ da ‘Gari Daya’ da kuma ‘Wani Hanin’ ya bayyana cewe, an yi kuskuren watsa cewa an kore shi daga gidan da yake haya, ya kuma rasa yadda zai yi, sannan yana neman kudin da zai biya kudin haya, hakan ba shi ne hakikanin halin da yake ciki ba.

Jarumin ya bayyana cewa ya shekara 21 a gidan hayar da yake ciki kafin aka tashe shi bayan ya kasa samo kudin da zai sayi gidan duk da an ba shi wa’adin shekara biyu don ya nemo kudin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 331

- Advertisement -

Ya ce, “Na shekara 21 a gidan hayar da aka tashe ni a ciki, ina zaune ne a gidan da nufin idan Allah Ya hore in biya shi, in ma Allah bai hore ba, to shi ke nan, ni dai maigidan bai matsa mini in rika biyansa kudin haya ba. Muna tare da shi, dan Jihar Nasarawa ne, sunansa Alhaji Yakubu Doma.

“Ya rasu a shekarun baya, inda bayan ya rasu ne, to ka san ’ya’ya da batun gado, sai suka zo za su sayar da gidansu, sai suka bukaci in saya, ni kuma ba ni da kudi, sai na kira wani ya saya a matsayin idan Allah Ya hore mani sai in mayar masa da kudinsa, sannan in ba shi karamar riba, inda ya amince ya ba ni shekara biyu, amma Wallahi Tallahi na nemi a yi mini alfarmar a saya mini gidan amma ban samu ba,” inji shi.

Bayan Karkuzu ya yi tarin tsufa ne, ya kuma gyara zama sai ya ci gaba da magana cikin murya kasa-kasa, “Shi kuma wanda ya yi mini wannan alfarma sai ya ga lallai yana so ya sayar da gidan, daga baya ya ce ya fasa sayarwa yana so in nemi wani gidan hayar ne domin zai rusa gidan don yin gini na zamani.”

Jarumin ya bayyana cewa shi da matarsa daya da ’ya’yansa bakwai – mata biyu, maza biyar, sun zauna a gidan bene mai hawa daya, mai yawan dakuna 11 har lokacin da ’ya’yansa mata biyu da suka yi aure, suka fita, inda ya ci gaba da zama da matarsa da kuma sauran ’ya’yansa maza a cikin gidan, inda daga baya ya zame masa dole ya tashi saboda ba shi da halin mallakar gidan.

“Daga nan sai na fita na kama haya a wani gidan mai dauke da dakuna uku da ke kan Titin Bauchi a garin Jos. Tafiya tana ta tafiya sai na ce kai, ni dai dan Najeriya ne, tun da al’amari ya zama haka sai na ce a sa a Facebook da Instagram, ko za a samu masu taimaka mini,” inji shi.

Da aka tambayi Karkuzu cewa ina batun cewa Atiku ya ce zai saya masa gida a Jos fa? Sai ya amsa da cewa “Billahillazi La’ilaha Illahuwa, ba mu yi wannan magana da Atiku ba, kuma Atiku Abubakar lokacin da muka sadu da shi, muna da yawa muka je wurinsa a Yola, ba mu taba samun Naira miliyan daya daga wajensa ba. Mu dai mun ci gaba da ayyukan tallata Atiku ne kafin nan gaba da muke sa rai za mu samu wani abu, ba mu taba magana da Atiku ko wani na kusa da shi ba don ya saya mini gida ba.

Ga batun cewa Gwamna Bindo Jibrilla zai saya masa gida fa? Sai ya ce ya taba koka wa Bindo don ya saya masa gida, amma har zuwa yanzu Gwamna Bindo bai yi komai ba.

Ya ce, “Na taba kokawa a gaban Gwamnan Jihar Adamawa, Bindo Jibrilla, na taba fada masa cewa ya saya mini gida, ita ma maganar ta tafi. Na ce masa ka taimake ni ka saya mini gida, amma dai har yanzu komai bai yiwu ba.

Ya kuma bayyana cewa ya kai wa Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong takardar da aka ba shi don ya tashi daga gidan hayar da yake ciki a da, shi ma ya yi alkawarin zai saya masa gida, amma bai saya masa ba.

“Na ba da takardar ce ta hannun Kwamishinan Kananan Hukumomi, Dayyabu Garga, bayan na hadu da Lalong lokacin da kaninsa ya mutu, wato na je yi masa ta’aziyya, sai ya ce mini ya samu takardarta daga kwamishinsa, sai na ce a taimaka, ya ce to zai duba, amma har yanzu bai gama dubawa ba.”

Karkuzu wanda ya shafe shekara 31 a harkar fim ya bayyana cewa babu wani dan fim da ya taimaka masa don ya sayi gida ko ya biya kudin haya. Ya ce, yadda ka ga duniyar nan a yanzu rayuwa ta gurbata, kuma kowa ta kansa yake. “Ga ’yan fim ba kowa zai taimake ka ba, a yanzu nawa ma ake samu a harkar fim? Ni ba fim nake shiryawa ko daukar nauyi ba, kira na ake yi in je in yi fim a ba ni Naira dubu 10 ko 20, ita ma in an ba ni ita, kafin wata dubu 20 ta sake shigowa sai na cinye ta har na ci bashin wata Naira dubu 20 din.

“Haka al’amuran suke tafiya, don haka wa za ka je ka ce ya taimake ka? Na rika bin su daya-bayan-daya, amma ba su taimake ni ba, ba zan kira maka suna ba, amma wadanda na nemi taimakonsu sun san kansu,” inji shi.

Daga karshe Karkuzu cikin kuka ya bukaci duk wani mai iko ya taimaka masa don ganin ya kai ga mallakar gida.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: