Kiwon lafiya

Shafawa mutumin da ya kone gishiri, danyen kwai na da matukar illa – Likita

Wani kwararren likitan kwakwalwa da kuna dake aiki a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas LASUTH Jamiu Umah ya ce ba daidai bane yadda wasu ke amfani da danyen kwai a matsayin mataki na faro wajen rage radadin zafin kuna.

Ya ce hakan da ake yi na da matukar illla a jikin mutum.

Jamiu Umah ya yi kira ga mutane da su guji amfani da jikaken gishiri, jikaken falawa,kullun koko, bakin mai da sauransu wajen saka wa sabon kuna wai don warkewa da wuri ko kuma ko don rage zafinsa. Ya ce kamata ya yi a dulmiya ko kuma a kwarara wa mutum ruwa mai sanyi ne maimakon haka.