A kwanan nan Barcelona za ta fara cin moriyar Sergio Aguero, bayan da ya fara atisaye ranar Laraba tun bayan da ya koma Barcelona da buga wasa a bana, yayin da kwantiraginsa ya kare a Manchester City a karshen kakar bara.
Mai shekara 33, wanda ya bayar da gudunmuwar da Argentina ta lashe Copa America a bana, ya ji rauni tun kafin fara wasannin kakar wasa ta bana, sai dai Barcelona wadda ke fuskantar kalubale a bana za ta yi murna da zarar dan kwallon ya fara buga mata tamaula.
Kungiyar tana ta shida a teburin La Liga, bayan da abokiyar hamayyarta, Atletico Madrid ta doke ta 2-0 – ta kuma sha kashi a wasa biyu na cikin rukuni a Champions League a bana sai dai tuni Aguero ya murmure wanda a ranar Laraba ya buga atisaye a karawar sada zumunta da UE Cornella. Yanzu dai ba a fayyace ko dan kwallon tawagar Argentina zai buga wa Barcelona gasar La Liga da za ta fafata da Balencia ranar Lahadi ba, sannan daga nan ta fuskanci Dynamo Kieb a Champions League, sai karawar hamayya ta El Clasico da Real Madrid za ta ziyarci Camp Nou ranar 24 ga watan Oktoba.
Add Comment