Labarai

‘Selfie’ na iya rusa Hajji – Limamin Ka’aba

Limamin masallacin Ka’aba, Faisal Ghazzawi ya bukaci mahajjata da su kaucewa daukar hotunan ‘selfie’ don gudun kar su bata aikin Hajjinsu.

Faisal Ghazzawi ya yi wannan kiran ne a hudubar da ya gabatar ta sallar Juma’a a ranar Sallah Babba.

 

Ya ce wasu mahajjatan kan dauki hotuna ne don sanar da al’umma cewa su na aikin Hajji da kuma fatan in sun koma gida a ce da su Alhaji ko Hajiya.

Hakan, in ji limamin zai iya kore ikhlasi daga cikin niyyarsu tare da haddasa riya, abubuwan da za su iya bata Hajji dungurungum.

fLimamin Ka’aba, Faisal Ghazzawi
Jigon hudubar dai shi ne darussan da Hajji ke koyarwa al’ummar Musulmi.

Daga cikin darussan da limamin ya zayyana akwai hadin kai, da kadaita Allah cikin bauta da addu’a da kuma neman taimako.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.