Labarai

Sarkin Kontagora Ya Rasu

Sarkin Kontagora Alhaji Sa’idu Ummaru Namaska ya rasu, Basaraken ya rasu yana da shekaru 87 a duniya, kuma ya shafe shekaru 47 yana sarauta. Babu cikakken rahoton musabbabin mutuwar, amma ya rasu ne a wani asibiti a birnin Tarayya Abuja.

Watanni uku da suka wuce ‘yan bindiga sun harbe a gidan gonar basaraken, wacce take kan hanyar Kontagora zuwa Zuru, inda suka harbe wasu ma’aikata tare da sace shanu. Zuwa yanzu iyalin Basaraken basu fitar da wata sanarwa ba kan mutuwar.

TARIHIN MAI MARTABA SARKIN SUDAN ALHAJI SA’IDU NAMASKA

An haifi Mai martaba Sarkin Sudan Alhaji Sa’idu Namaska, a garin Kontagora dake Jihar Neja a yanzu. A ranar 31st, ga watan disamban shekarar 1937. Sarki Saidu Ɗa ne ga Umaru Sarkin Kudu. Umaru Sarkin Kudu wanda yake ɗa ga Umaru Nagwamatse wanda shi ne Sarkin farko kuma wanda ya kafa ƙasar Kontagora.

Sarki Saidu basarake ne kuma jika ga Usmanu Danfodio. Malami ne na addinin Musulunci, kamar yadda musulunci ne ya gina gidan su.

Yayi makarantar Elementary a tsakanin shekarun 1945 zuwa 1950. Sannan a shekaran 1950 ya shiga Bida middle school har zuwa 1953.

Ya fara aiki a matsayin dan doka. daga baya kuma ya koma yana aiki da Native Authority a shekarar 1954 a matsayin jami’in kula da gandun daji. A shekarar 1957, Alhaji Saidu Namaska ya samu karin girma a wurin aiki. Daga bisani ya zamo Alkalin Area court a garin Salka a Shekarata 1968.

A shekaran 1971 ya koma da aikin sa a garin Mahuta, yankin masarautar Zuru dake Jihar Kebbi a yanzu.

Sarki Saidu ya tafi makaranta dan qarin ilimin shari’a a Institute of Administration, Zaria a 1962 inda ya gama da kyakkyawan sakamako na ma’aikatar shari’a. Bayan nan kuma ya qara yin wani kwas a wannan makarantar dai da ke Zari’a a wani mataki na gaba, ya kuma sake gamawa da sakamako fiye da na farko a shekaran 1972.

Bayan shekara biyu Sarki Saidu ya gaji Sarki Mu’azu a karagar mulkin Kontagora a shekarar 1974. Sarki Saidu shine sarki na shida a jerin sarakunan masarautar na Kontagora. Kuma shi yafi kowani sarki daxewa akan mulkin masarautar. Wanda ya kwashe shekaru 47 akan mulki. Kafin rasuwar sa shine mataimakin shugaban majalisar sarakuna na Jihar Neja.

Masarautar sa ita ce ta 11 a jadawalin masarautu a Arewacin Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: