Sarkin Katsina Ya Kori Hakimin Kankara Bisa Samunsa Da Hannu Dumu-dumu Wajen Taimakawa Barayin Daji

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Magaji Sani Sabuwa

Mai Martaba Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir ya kori hakimin gundumar Kankara bisa zarginsa da hannu wajen hadin baki da ‘yan ta’adda domin aiwatar da ta’addanci a jihar da ma wasu jihohi dake makwaftaka da su.

Sakataren Masarautar, Bello Ifo ne ya bada tabbacin korar Hakimin a yayin da yake zantawa da wakilin Freedom Radio a Katsina, Yusuf Jargaba game da lamarin a daren Jumu’ar nan.

A cewar Ifo, Masarautar ta dauki matakin korar Yusuf Lawal ne bayan da kwamitin bincike da Masarautar ta kafa akan hakimin a kwanakin baya ya mika mata rahoto, inda kuma kwamitin ya tabbatar da zarge-zargen da akeyi masa na hadin baki da yan ta’adda.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

Tuni dai Masarautar tace ta fara shirin maye gurbinsa da wani hakimin.

Idan za’a iya iya tinawa dai a ranar 30 ga watan Afrilu ne dai, Sarkin Katsina ya bada umarnin dakatar da Hakimin Kankarar, kuma ya kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar zarge-zargen da ake yi masa na taimakawa Yan ta’adda.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: