Labarai

Sarkin Karaye ya sake nada dan uwan Kwankwaso a sarauta

Sarkin Karaye ya sake nada dan uwan Kwankwaso a sarauta

Mai martaba sarkin Karaye, Dakta Ibrahim Abubakar II, ya nada Alhaji Umar Musa Kwankwaso, a matsayin majidadin Karaye, wanda dan uwa ne ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanarwar nadin na kunshe cikin wata wasika mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na masarautar, Haruna Gunduwawa ya fitar, inda yace za ayi bikin nadin nasa tare da wasu mutane 11 da sarkin ya nada su a sarauta, a ranakun 19 da 26 ga watan da muke ciki na Mayu.

#NasaraRadio

#AmanarTalaka

14/5/2023