“Sarakunan gargajiya na da hannu a rikicin arewacin Najeriya”


0 146

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali ya bayyana cewa, sabbin bayanan sirri sun nuna cewa, wasu manyan sarakunan gargajiya na da hannu kashe-kashen da ake fama da su a wasu yankuna na arewacin kasar.

A wata sanarwa da ya aika wa Jaridar Premium Times, Ministan ya ce, sun gano cewa, sarakunan gargajiyar da ba a bayyana sunansu ba, na da hannu a hare-haren ‘yan bindigar, amma ya lashi takocin cewa, za su fuskanci hukunci.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Ministan ya bukaci al’ummar jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da sauran sassan arewacin Najeriya da su tashi tsaye wajen bayar da goyon baya ga yunkurin gwamnati na magance tashin hankalin, lura da cewa, sojojin da ke filin-daga ba za su iya yakar maharan su kadai ba.

Kazalika har yanzu kasar na fama da matsalar Boko Haram a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.

 

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.