Kannywood

Sani Danja J Martin Da P Square Zasuyi Wa A Abuja

Mawakin turanchi kuma jarumin fina finan hausa Sani Danja ya shirya tsaf dan kawo maku shagalin sallah karama a bana. amma wannan karon Danja ya canja salon shagalin na shi. domin shida fitattun wakan turancin nan J, Martin, da P Square zasu yi shagalin sallah a Wuse II Abuja.

 

Zasu dauki tsawon kwana uku suna gudanar da shagalin sallah. a irin tsare tsaren da sukayi ciki harda gasar rawa wadda za’a gudanar tsakanin mawakan kudanci dana Arewacin kasar nan.

 

Sani Danja shine mawakin da zai wakilci tawagar masu waka da rawa na Arewa. Shi kuma J Martin zai wakilci kudancin Nigeria.

 

Kudin shiga naira 1000 kacal. kuma abincin da za ka ci kyautane, ba ko sisin kwabon ka. kuma akwai kyautar Album Maisuna ‘Africa’ wanda za’a baka. duk idan ka biya kudin shiga. za’a fara wasa tun daga yau da misalin 4:30 pm zuwa 10:30 pm.

 

Allah ya bada ikon zuwa.