Get New DJ Mixes
Wasanni

Sanchez zai dawo kan ganiyarsa — Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger, ya ce, Alexis Sanchez ba zai samu matsalar dawowa kan ganiyarsa a Arsenal ba, bayan da bai ji dadin halin da ya tsinci kansa a lokacin kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon Turai ba.

A ranar da za a rufe kasuwar ‘yan tamaular ne, Sanchez dan kwallon Chile mai shekara 28 ya kusa komawa Manchester City, sai dai kuma Wenger bai yi wani kokwanto game da tunani da kuma shawarar Sanchez din ba.

 

Arsenal ta amince da yarjejenyar fam miliyan 60 da Man City sai dai kuma ya danganta da shawarar da suka yi na daukar Thomas Lemar, wanda suka yi shawarar ya zauna a Monaco.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.