Sanatoci Sun Karbi Cin Hanci Domin Amincewa Da Peace Corps
Domin rattaba hannu a kudirin Peace Corps Sun yi Wal-Ba-Ni-Wal-Baka tsakanin su da jagororin Peace Corps. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, sai da kowane Sanata aka ba shi tikitin daukar mutum bakwai-bakwai gami da ‘yan kudade kafin su goyi bayan kudirin ya zama doka.
Jiga-jigai daga cikin sanatocin sai da aka yayyafa musu ruwan tikitai kimanin 500 na daukar ma’aikata sannan suka bayar da kai bori ya hau.
Add Comment