Labarai

Sanata Malam Uba Sani Ya kaddamar Da Katafaren Dakin Kwanan Dalibai A Makarantar ‘Yan Mata Ta Giwa

A jiya Lahadi ne Sanatan Kaduna ta Tsakiya Malam Uba Sani, ya kaddamar da katafaren dakin kwanan dalibai na mata a makarantar kwana ta ‘yan mata dake garin Giwan jahar Kaduna. Sanatan wanda ya gina dakin mai dauke da gadaje guda 110, ya ce ya gina dakin ne don kara wadata daliban da dakunan kwana.

Taron ya samu halartar Shugaban karamar hukumar ta Giwa Hon. Abubakar Shehu Lawal Giwa, tare da ‘yan majalisun jiha da na tarayya.

Daga nan Sanatan ya zarce zuwa sansanin ‘yan gudun hijira dake cikin garin Iyatawa, don bayar da tallafi ga wadanda ibtila’in rashin tsaro ya korosu daga garuruwan su.

Daga karshe mutanen garin sun yi addu’o’i da fatan alkairi ga Sanata Malam Uba Sani.

Daga Sunusi (D) Danmaliki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: