Daga Muhammad Adamu Yayari
A cigaba da kokarinsa na ganin ya Inganta harkar lafiya na Al’ummar da yake wakilta, jagoran siyasar jihar Gombe Sanata Mohammed Danjuma Goje ya mika kayayyakin aikin jinya ga asibitocin Kalshingi, Akko gari, kwadom da Shinga.
Jagoran Wanda ya samu wakilcin Alh. Adamu P.A da Alh. Danjuma Babayo ya bayyana cewar kayayyakin aikin jinya ya kawosu ne musamman Don tabbatar da kudirinsa na samar da ingantacciyar kulawa ga harkar lafiya na Al’ummar da yake wakilta.
A nata jawabin, Malama maryam Usman dake kula da asibitin Akko gari tace irin wadannan kayayyakin jinya da Jagoran ya samar musu a asibitin basu taba amfani da irinsu ba asibitoci kanana, suna ganin irin kayayyakin ne a asibitoci manya na cikin gari.
Kayayyakin jinya sun had’a da Numfashi, Gadaje, injin gwajin jini, injin Gwajin sugar, Allurai, injin gwada nauyi, Safar hanu da sauransu.