Sanarwa Mai Mahimmanci Daga Rundunar Sojin Najeriya

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

SANARWA MAI MUHIMMANCI DAGA RUNDINAR SOJIN NIGERIA

Daga Assalafy

Talla

Rundinar sojin Nigeria tana sanar da al’ummar Nigeria masu amfani da kafofin sadarwa na zamani cewa rundinar ta shirya tsaf wajen daukar matakin a kan wadanda suke yada hotona da video na farfaganda irin na ‘yan ta’adda wanda yin hakan tamkar suna taya ‘yan ta’adda yada farfagandarsu ne

Rundinar sojin tace akwai kundin doka wanda ya tanadi hukuncin laifukan da ake aikatawa ta kafar yanar gizo (Cybercrimes) kundin dokar yayi bayani tun daga sashi na 24(1)(a),(b) da kuma sashi na (2)(a),(b),(c)(i),(ii) Cybercrimes (Prohibition & Prevention etc) Act, 2015

Daga yanzu rundinar sojin Nigeria zata fara bin diddigin masu yada hotuna da videon farfaganda na ‘yan ta’adda za’a cafkesu a hada case file dinsu sannan a gurfanar dasu a kotu don su fuskanci hukunci bisa doka

Talla
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Rundinar sojin Nigeria ta kara da cewa abin bakin ciki ne da takaici yadda wasu suka dinga yada hotunan karya da video na farfaganda akan harin da ‘yan ta’adda sukayi a sansanin sojoji dake kauyen Metele jihar Borno, wannan wani yunkurine ne na cin amanar tsaron ‘kasa wanda ba za’a lamunce da hakan ba.

Jama’a a kiyaye wajen yada hotunan karya da video, duk kafar sadarwa da kake amfani da ita jami’an tsaro da suka kware a Cyber Security zasu iya bin diddigi a iso har inda kake, idan an kamaka zakayi bayanin sahihancin videon ko hoto da kuma inda ka samo hoton ko videon, kaga hakan zaiyi implicating mutane da yawa, don haka a kiyaye a dena biye wa ‘yan shi’ah da ‘yan ta’adda

Wallahi cikin hotunan da naga ‘yan shi’ah sun yada har da wanda ‘yan ta’adda sukayi hari a barikin Giwa dake Maiduguri a shekarar 2014, da hotunan harin da Alshabab tayi a Somalia a shekarar 2012, da hotunan harin da BH sukayi a shekarar 2017 a wani kauye a Jihar Yobe, amma sukayi ta yadawa suna cewa harin Metele ne da ya faru ranar Litinin da ta gabata

Allah Ka kawo mana karshen tsageru ‘yan shi’ah da ‘yan uwansu ‘yan ta’adda, makirci da farfaganda da suke kullawa Allah Ka sa ya kare a kansu

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: