Samfuran Kalaman Soyayya

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zuciyata tana ta faman jiranka burinta kawai ta ganka sannan idanuwana sun kasa ganin kowa ba abin da suke son gani sai kykyawar fuskarka abin alfaharina .

Kaunarki ta mamayemini Dukkannin sassan ilahirin jikina. Tabi jini, tsoka, zuwa bargon ashina. Domin zuciyata ita ce ma’adanin surrikan tinaninki a kodayaushe, Masoyiyata Tabbas zuciya wata aba ce waddda takan sa gangar jiki rashin amfani idan ba ta samu abin da take so ba ban san sonka ya yi nisa haka a zuciyata ba sai da Na zauna ina tunaninka kawai na ga hawaye Na zuba daga cikin idona hakika kaunarka ta kai mutukar kurewa a cikin raina .

Talla

Na kasance ma’abocin soyayya Lokaci na shudewa soyayyarki na karuwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da za ta iya canja matsayin ki a wajena.

Ni fa ina ganin da akwai wata mace da zata ganka ta kalle ka tabbas zan iya sawa ayi mata duka saboda tana kallon muradin raina nifa saboda tsantsar Kaunarka bana bacci sai naga fuskark haka zalika da ita nake fara farkawa daga bacci.

Ka da ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato *Ina SonKa* hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai ba shi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada, Ina son ki.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 35

Zan fi kowa dacewa idan kika rike Kaunar da ke tsakaninmu nai maki wata wani tanadi duk sanda kika kasance uwar ‘ya’yan mu zuciyata za ta kasance mai yabonki da kuma nuna maki kulawa wanda uwa take bawa danta, Ki kasance tawa ta har abada ♡Idan kowa haka ta samu a tsakaninmu ba abin da za mu nema a cikin wnnan duniyar saboda ya cika mana burin mu sai dai fatan mugama da dunia lafiya……   Ameen Sarauniyata.

Ke kadai nake kallo bana kallon kowacce mace saboda  duk sanda idona zai ci karo da wani abu to kyakyawar fuskarki ce mai cike da kyakyawar fara a tare da iya kallon abin kaunarta. Lallai na yi dace da samun Sarauniya, duk sauran matan bayinki ne. Ni ma daga kai babu wani namiji da kwayar idona ke iya gani ya burgeta sai kai nifa ina ganin duk wata mace na fita dacewa sai dai ta yi fatan Allah ya ba ta i-nawa amma ni kam na yi gaba saboda nayi gamo da burin zuciyata.

Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa duk-kanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba, Ina son ki fiye da gwal ko kud’i.   Ai abin da kaga yana zuciya ba ka iya furtashi gaskia wannan karamin abune nifa tawa soyayyar babu abinda baki zai iya kwatantashi da shi sannan babu wani  mizani da zai iya auna ma auninta sai dai  daga zuciya zuwa zuciya wnnan kadai shi ne zai ji abin da take ji game da kaunarka .

A lokacin da ki ka ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin daya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada, ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a maboya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.   Nima Ina fatan za ka ci gaba da kulamin Da ‘yar jaririyar zuciyata kamar yadda nima nake bawa taka kykyawar kulawa I edtremely lobe you.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: