Samar Da Makarantun Hadin Kai, Shine Hanyar Samar Da Zaman Lafiya A Jihar Kaduna -Sarkin Zazzau

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Samar Da Makarantun Hadin Kai, Shine Hanyar Samar Da Zaman Lafiya A Jihar Kaduna – Sarkin Zazzau

Mai Martaba Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris, ya bayyana cewa matukar ana son a dawo da zaman lafiya da hadin kan al’ummar jihar kaduna, akwai bukatar gwamnatin jihar ta samar da Makarantun hada kai ( UNITY SCHOOLS ) wanda hakan zai bayar da dama ga dalibai su rinka samun fahimtar juna tun suna karatu.

Talla

Sarkin Zazzau, ya bayar da shawarar ne a yayin da yake jawabi a taron da shugaban Kasa Muhammadu Buhari, yayi da Sarakuna da malaman addinin kirista da musulmi a kaduna domin jajanta musu bisa rikicin da ya faru a jihar kwanan baya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Dakta Shehu Idris, yace akasarin wadanda ake Amfani Da su wajen tayar da rikici Matasa ne, wadanda kuma suke da karancin ilimi da fahimtar zamantakewar juna, inda ya ce idan gwamnatin jihar ta samar da irin wadannan makarantu na Hada Kai babu shakka Dalibai zasu San darajar juna da fahimtar addinin juna ta mu’alamar yau da kullum. Sarkin ya bayar da misalin, gudummawar da Makarantun Hada Kai suka bayar wajen Hada Kan ‘yan Arewa a shekarun baya, Yana Mai cewa mafiya yawan manyan kasar Nan sun halarci irin wadannan Makarantun ne, acewarsa, Akwai Bukatar Gwamnatin Kaduna da ta Kara samar da Makarantun a fadin jihar domin dawo da zamantakewar al’ummar musamman ma dalibai matasa.

Sai dai Sarkin ya nuna takaicinsa dangane da yadda yanzu a jihar kaduna, mabiya addinin kirista da musulmi suka ware unguwanni su Wanda Hakan a cewarsa Abin takaici ne da damuwa matuka.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: