Rahotanni na cewa shahararren dan wasan kasar Masar, Mohammed Salah yana neman Liberpool ta amince za ta rika biyansa fam dubu dari biyar 500,000 duk mako
kafin ya sanya hannu a wani sabon kwantiragin ci gaba da yi mata wasa.
Kwaniragin dan wasan da Liverpool zai kare a shekarar 2023, kuma kungiyar ta zaku ta shiga sabuwar yarjejeniya da dan wasan a daidai lokacin da Real Madrid da Barcelona ke nemansa.
Amma wani sabon rahoto na cewa Salah na neman a rika biyansa rabin miliyan na kudin fam din Ingila duk mako domin ci gaba da zama Liverpool kuma kwanan nan Salah ya ce a shirye ya ke ya karkare kwantiraginsa da Liberpool, amma yana nema ya zama dan wasan da ya fi kowa daukar albashi a kungiyar.
A ranar Lahadin da ta gabata ya saka kwallo 3 rigis a ragar Manchester United, a wasan da Liverpool ta lallasa ta 5-0 a Old Trafford, sannan Salah ya kafa tarihin zama dan wasan Afrika da ya fi zura kwallo a gasar firimiyar Ingila a tarihi, inda a yanzu ya zarta Didier Drogba na Ivory Coast.
Yanzu haka Salah dan asalin kasar Masar ya jefa kwallaye 107 a gasar ta Firimiyar Ingila, yayin da a wasansu da Manchester United ya ci kwallaye uku shi kadai,. abin da a Turance ake cewa ‘Hat-trick’ sannan Salah ya sha gaban Drogba da ya buga wasa a Chelsea da kwallaye uku.
Sauran ‘yan wasan Afrika mafiya yawan kwallaye a gasar ta firiyar Ingila sun hada da Sadio Mane mai kwallaye 100, sai Emmanuel Adebayor mai kwallaye 97, yayin da Yakubu Ayegbemi ke da kwallaye 95.
Add Comment