Sakon Sheik Zuwa Ga Yan Shia Akan Zabe

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Bilya Hamza Dass

Maganganu sun yi ta yawo kan yiyuwar shigan ‘yan Shi’a babban zabe me zuwa a kasar nan da za’a fara ranar 16 ga watan biyu. Wanda a baya ‘yan shi’an sun kasance suna kauracewa yin harkar zaben a shekarun baya su zaba ko su shiga a zabesu. Amma cikin kwanakin nan maganganu sun tsananta kan mabiya shi’a wandanda gwamnati me mulki ke tsare da jagoransu shekaru 3, kanyiyuwar su shiga ayi dasu.

Talla

Wasu rohatanni sun bayyana cewa mabiya shi’an da suke da yawa a wasu daga jahohin arewacin kasar nan wanda ana fadin adadinsu yakai miliyoyi zasu bada dukkan kuri’unsu ga Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin Jam’iyar Adawa ta PDP. Daga bangaren jami’an tsaro kuwa suna raba takarda ga hukumomi cewa mabiya shi’an suna shiri tada hargitsi a lokacin zaben, inda tuni mabiyan shi’an suka karyata hakan tare da jan kunne.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

A ranar Asabar 26/01/2019, wasu daga makusantan Shaik Ibraheem Zakzaky sun ziyarce shi a wajan da ake tsare da shi sannan ya yi magana kan zantukan da ake yadawa kansu akan zaben yana cewa “To mu muna zabe ne? Ina ruwan mu da zaben su. Kuma ma mu ai ba’a sanmu da hargitsi ba, idan ma haka ne. Su kansu wannan al’ummar sun yi mana shaida akan cewa mu ba masu hargisti bane” inji shi.

#Rariya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: