Daga A’isha Usman Golden Damaturu, Yobe
A koda yaushe nakan cika da mamaki idan na ga yadda mutane ke zumudi akan Buhari.
Saboda idan na waiga gefen Buharin, shi ko kadan ba ya yi don talaka.
Kuyi hakuri idan kalamai na sun yi kaushi da yawa, domin bana nufin cin mutuncin kowa.
A sanina akan so mutum ne saboda kyautatawarsa ga mutane.
Ya kamata ‘yan uwana matasa su farka daga baccin da suke.
Ku sani a wasu kasashen fa matasa karatunsu kyauta ne, kuma har ma akan kara musu da alawus, amma bayan hawan Buhari saida aka kara kudin kowane mataki na ilimi, ma’ana masu hali su yi, dan talaka kuma ko oho.
Kowa ya san yadda abinci ya yi tashin gwauron zabi a kasar nan, komai ya linka kudinsa.
An cire tallafin mai. Ga shi tsaro da ake ta babatu ya kawo karshe, Wallahi ba gaskiya bane.
Saboda mu a nan Yobe ba Buhari ne ya dawo da mu gida ba, a gidajen mu muka zabe shi.
Kuma dama tun kafin Buhari ya zo karfin Boko Haram ya ragu sosai.
Kuma har yanzu wanda suka fito daga kauyuka irin su Baga da Konduga, har yanzu fa ba su koma gidajen su ba, suna sansanin gudun hijira.
Idan tsaro ya inganta me ya hana su koma gidajensu?
Daga kin gaskiya sai bata. ‘Yan uwana matasa mu yi wa kanmu adalci so ba hauka bane.
Abgaskiya hawan Buhari mulki babu abinda ya tsinanawa Nijeriya sai ma jefa mu cikin kuncin rayuwa da yayi. Don haka ya rage namu.
Yanzu Nijeriya muna bukatar wanda zai samarwa talaka aikin yi, bunkasa kasuwanci, ilimi ga talaka cikin sauki, kyautata yanayin kasa, bunkasa harkar noma, isashiyar wutar lantarki, farfado da masana’antu, kyautata diflomasiyya, ingantattun hanyoyi, uwa uba talaka ya samu saukin rayuwa, da kokarin hada kan ‘yan kasa da sauransu.
Hakan kuwa ba za ta samu ba sai muns amu shugaba mai saukin kai mai gogewa cikin ayyukan jama’a, mai karbar shawara, mai waigawa kowane gefe kafin ya zartar da hukunci, uwa uba mai tausayin talaka.
Amma gaskiya Buhari ya gaza.
Mu cire son zuciya mu fadi gaskiya.
Sannan akwai wani ramin halaka da magoya bayan Buhari ke fadawa na danganta wa Buhari alheri su dangantawa Allah sharri.
Kuma suna debe tsammani a gurin Allah na cewa babu nagartaccen bawa da Allah zai iya ba su a matsayin shugaba sai Buhari.
A gaskiya wannan kuskure ne.
Da fatan za a gyara, ina kuma fatan masu karatu za ku yimin adalci akan tsokacina, amma 2019 dole mu sake lale saboda talaka ma yana so ya ji dadi kamar kowa.
Amma meye amfanin badi ba rai?
Mu koma ga Allah mu roki zabinsa ba na mu ba.
Allah ka ba mu wanda ke son mu, ba wanda muke so ba, ka ba mu wanda yake tausayin mu ba wanda muke tausayi ba.
Amin.
Add Comment