Sake Zaben Buhari Ya Zama Wajibi Ga `Yan Najeriya Saboda Wasu Dalilai Guda Biyar –Ribadu

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohon shugaban Hukumar EFCC, Nuhu Ribadu ya bayyana wa dubban magoya bayan sa a garin Yola cewa lallai shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci zarcewa a 2019 domin ci gaba da ayyukan ci gaba da yake yi a kasar nan.

Ribadu ya ci gaba da cewa da ga wannan rana ta Litini, ya mika wa Kamfen din Buhari gaba daya motoci, ofisoshi da kayayan aiki da yayi amfani da su a wajrn neman takarar gwamnan jihar Adamawa da yayi.

Talla

Bayan haka ya zano wasu dalilai da ya ce hujjojine ga duk mai kaunar Buhari da ma ‘Yan Najeriya su sake zaban sa a karo na biyu musamman ga mutanen yankin Arewa maso Gabas.

1 – zaben 2019, zabe ne da zai banbanta tsakuwa da aya. Zaben kauce wa irin fuskokin da suka rugurguza kasar nan a rungumi gwamnati mai adalci.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

2 – Inganta wa da samar da tsaro mai nagarta kamar yadda ake dandanawa yanzu musamman a jihar Adamawa.

3 – Ayyukan ci gaba da ake samu a karkashin wannan gwamnati musamman a sassab jihar da ba ataba samun irin haka nuni ne cewa wannan gwamnati da take da muradun ci gaban mutanen wannan jiha.

4 – Manoma suna ta ragargazar romon shirin tallafi da gwamnatin tarayya ta ke ba su domin bunkasa ayyukan su.

5 – Yaki da cin hanci da rashawa da fatattakar barayi ya yi matukar tasiri a wannan kasa.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: