Labarai

A sake fasalin kasar Najeriya kowa ya kama gaban sa – Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina kuma tsohon kakakin majalisar wakillan Najeriya Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa shi fa yana goyon bayan a sake fasalin kasar nan ta Najeriya amma dai kafin hakan ya kamata ayi laakari da wasu ababe idan anzo yin hakan.

Gwamnan ya bayyana wa wakilin majiyar mu cewa ko shakka babu akwai bukatar a rage wa gwamnatin tarayya dake a tsakiya yawan karfi ko kuma ayyuka ta, amma kuma a yayin yin hakan sai kuma anyi la’akari da wasu abubuwa da dama.

A samu cewa Gwamnan na Katsina dake a Arewa maso yammacin Najeriya ya kuma ce kowane bangare na gwamnatocin tarayya da na jihohi na da irin kalar nauyin da ya kamata a bashi ya dauka domin kowannensu suna da hanyoyin da za su warware kalubalan dake gabansa cikin ruwan sanyi.

Daga nan ne kuma sai Gwamnan ya bada misalin cewa ba abinda ya hada gwamnatin tarayya da gina rijiyar burtsatse, ko kuma makarantar firamareda da dai sauran wadannan kananan ayyukan.

 

Source Mikiya Hausa