Labarai

Sake Farfado Da Nijeriya Abu Ne Mai Yiwuwa, Inji Osinbajo

Daga Sulaiman Ibrahim,
Duk da yanayin matsin tattalin arzikin da ake ciki yanzu da kalubalen da ake fuskanta, samar da yanayin habaka tattalin arziki, kawar da talauci, habaka dan Adam da gina kashin bayan abubuwan more rayuwa a Nijeriya mai dorewa abu ne mai yiyuwa, inji Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo (SAN).

Don haka Osinbajo ya umarci dukkan bangarorin gwamnati da abokan hulda da su mai da hankali, su hada kai wajen cimma burin da ake son a cimma – samar da ingantattun rayuwa da ingantattun ayyuka ga ‘yan Nijeriya, musamman matasa.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Laolu Akande ya fitar, Farfesa Osinbajo ya bayyana wadannan ra’ayoyin ne yayin da yake bude taro na 20 na Kwamitin Shirye -shiryen hadin gwiwa da Majalisar Kasa kan Shirye -shiryen Ci Gaban a Maiduguri, Jihar Borno.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: