Sakamakon Yajin Yan Adaidaita Mawaki Rarara ya Fito da Motoci Domin Daukar Mutane Kyauta a Kano

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

Daga Hafsat Abdullahi

Sakamakon yajin aikin masu Adaidaita sahu a jihar kano, shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bada umarnin fito da motocin kungiyarsa ta kwallon kafa domin su rika daukar mutane kyauta.

 

Kadaura24 ta rawaito al’umma da dama suna ta faman tafiyar kasa sakamakon yajin aikin da ‘yan adaidaita sahu suka fara yi tun a ranar litinin din data gabata.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 342

Cikin wani bidiyo da mawakin ya wallafa a shafin kamfaninsa yace Motocin an fito da Motocin ne domin taimakawa al’umma sakamakon mawuyacin halin da suka shiga saboda yajin aikin yan adaidaita sahu.

” An fito da Motocin ne domin su dauki mutane musamman dalibai da zasu tafi ko zasu koma gida kuma kyauta ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba”. Inji Rarara

Al’umma da dama dai suna wahala sosai sakamakon yajin aikin yan adaidaita sahu, wanda ya faru sakamakon rashin fahimtar data shiga tsakanin Hukumar Karota da Yan adaidaita sahu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.