Sai Yaushe Gwamnatin Buhari Zata Damu Da Damuwar Matasa?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Bashir Abdullahi El-bash:-

Kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zabe a (2015), ba za ka taba yarda ba idan wani ya rantse maka da Allah cewar Matasan da su ke kwakwazo da kakatu a (New Media) kan Baba Buhari za su zama abin wofintarwa a gwamnatin Buhari ba.

Talla

Ba don komai ba, sai duba da yadda kowa ya gamsu dari-bisa-dari Shugaba Buhari mutum ne mai son ganin al’umma musamman Matasa sun ginu sun zauna da kafafuwansu kan dogaro da kai.

Sai dai kash! Abin kunya abin takaici, yau ana daf! Da cinye shekaru hudu (4) na zangon farko na gwamnatin Buhari, har ma an fara shirye-shiryen tunkarar zabe a karo na biyu, amma babu wani Matashi mai rajin kare muradu da manufofin gwamnatin Buhari a sabbin kafafen sadarwa na zamani (New Media), da za a daga a kalla a matsayin wanda gwamnatin Buhari ta yi wa silar zama wani abin alfahari kan dogaro da kai.

Tabbas mun sani, ba mu jajirce wajen kafuwar wannan gwamnati domin ta wawuro mana dukiyar al’umma daga cikin baitulmali ta ba mu ba, duba da manufofinta na yaki da cin-hanci da rashawa, sai dai mun kyautata mata zaton za ta iya yi mana wani tsari na musamman da zai taimaka mana wajen kafuwa da duga-duganmu, ta yadda hakan zai kara taimaka mata wajen samar da ayyukan yi ga dumbin Matasan da ba sa aiki.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 14

Sanin kowa ne, akwai bambanci tsakanin hakkin dan ‘yan ‘kasa, da kuma hakkin wadanda su ka ba da gudunmawa wajen kafuwar gwamnati. Duk dan ‘kasa ya na da hakki gwamnati ta kyautata masa ta kuma kula da damuwarsa, haka zalika, ba laifi ba ne ga duk wata gwamnati ta yi wani tsari na musamman da za ta taimakawa wadanda su ka taimaka ta kafu ba.

Domin ko sarkin da ya yi mu, (Allah), tun a Duniya ya fifita wadan su ka taimaka wajen kafuwar addininsa a doron ‘kasa fiye da wadanda ba su taimaka ba, kenan a babin Siyasa ma hakan ba laifi ba ne.

Misali, Ni Bashir Abdullahi Elbash, ina da kamfani nawa na kaina da na ke gudanar da ayyukan yada labarai (Online),

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: