KannywoodKwana Casa'in

Sahabi Madugu Ya Magantu Akan Aibata Matarshi da Wasu Daga Cikin Mutane Keyi

Aliyu Hussain wanda akafi sani da Sahabi Madugu a cikin shirin Kwana Chasa’in ya magantu akan aibata Matar shi da wasu daga cikin mutane sukeyi wacce aka daura musu  aure a satin da ya gaba.

Da yawan mutanen dake ta yada hoton Matata Hassana har suke kokarin aibata halittar ta, sun san ni bayan dana zama SAHABI a cikin shirin Kwana Chasa’in, basu sanni a lokacin da nake Aliyu ba….

Alhamdulillah Hassana ta kaunaceni a lokacin da ni ba kowan kowa bane, lokacin da hatta a unguwarmu ba kowa bane yasan dani, don haka ne nima na rike alkawarin ba zan iya rabuwa da Hassana ba, koda kuwa me na zama a wannan duniyar…

Akwai Yan’mata masu yawa da suka nuna kauna gareni a yanzu bayan dana zama SAHABI, to amma anya kuwa Aliyu suke so, kodai Sahabin Kwana Chasa’in suke so…?

Soyayya ta tsakani da Allah Hassana ke yimun, haka nima dai soyayya ta gaskiya nake mata, ni da ita ba kyale kyale muka kalla ba…

Ni Aliyu Hussain ina cigaba da yiwa Allah godiya sakamakon kyautar Mata Hassana daya bani, ina kallon kyawunta kwatankwacin sarauniyar kyau ta duniya, ina addu’ar Allah ya hadani da Matata Hassana a aljanna…..

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: