Kannywood

Sadiq Sani ya sake zama jarumin jarumai


Anyi bikin karrama fitattun jarumai a masana’antar Kannywood 

Fitaccen dan wasan Fina-finan Hausa, wato Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya lashe kyautar jarumin jarumai a karo na biyu a jere.

An sanar da hakan ne a wajen taron karrama ‘yan Fim da aka yi ranar Asabar da daddare a Abuja, babban birnin Najeriya.
Dan wasan Fim din ya lashe kyautar ne saboda rawar da ya taka a Fim din “Bayan Duhu”.
Kazalika Nafisa Abdullahi ce ta yi nasarar zama jarumar jarumai a bangaren mata sakamakon rawar da ta taka a Fim din “Baiwar Allah”.
Sauran wadanda suka yi nasara su ne Sulaiman Yahaya Bosho, wanda ya lashe kyautar “Dan wasan Barkwanci”, yayin da Maryam Baba Asin ta yi nasara a matsayin “jarumar jarumai a rukunin kananan yara” sakamakon ficen da ta yi a Fim din “Basma”.
Ali Gumzak ne ya lashe kyautar “Gwarzon Darakta “, yayin da Haruna Talle Maifata ya lashe kyautar “Dan wasan da ya fi mugunta”.
Lawan Ahmed ne ya yi nasara a fannin “Dan wasan da ya taimakawa babban jarumi” a Fim din “Da’iman”, yayin da Fati Shu’uma ta yi nasara a matsayin ” ‘yar wasan da ta taimakawa babban jarumi” a Fim din “Basma”.
Umar M. Sheriff ne ya zama “Gwarzon mawaki”.
Fitattun jarumai da ministoci da kuma masana na cikin wadanda suka halarci bikin.
Ga dai abin da wasunsu ke cewa bayan da aka basu wannan lambar yabo.
http://ichef.bbci.co.uk/news/ws/640/amz/worldservice/live/assets/images/2016/03/06/160306143423_kannywood_dadinkowa_awards_640x360_salisu_nocredit.jpg

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.