Labarai

Sace Dalibai Akalla 100 Ya Tilasta Rufe Makarantu 13 A Kaduna

Daga Abubakar Abba, Kaduna
Biyo bayan barazanar tsaro da sace yara ‘yan makaranta sama da 100 a makarantar Cocin Bethel Baptist da ke Kujama a karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, Hukumar Kula da Ingancin Makarantu ta Jihar ta umarci makarantu 13 da ke yankunan da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga su gaggauta rufe su.

A cikin wasikar da Darakta Janar na hukumar, Umma K. Ahmed ta aike wa masu mallakar makarantun da abin ya shafa, an bayyana cewa,“Bayan bayanan da suka isa ga hukumomi game da barazanar tsaro a makarantar Baptist Baptist High, Damishi, an yi taro tare da Kungiyar Masu Mallakar Makarantu Masu Zaman Kansu (NAPPS) da wasu manyan masu ruwa da tsaki a ranar Litinin 5 ga Yuli, 2021 inda aka cimma kudurin cewa ya kamata makarantu masu zaman kasu su rufe daga ranar Litinin 5 ga Yulin 2021.”

Wasikar ta yi gargadin cewa duk mai makarantar da ya nuna taurin kai ya ki rufe makarantarsa a yankin da babu wani isasshen tsaro, zai dandana kudarsa.

Makarantun da abin ya shafa dai kamar yadda rahotanni suka nunar sun hada da: Faith Academy, da ke kan titin Kachia daura da Jakaranda, Deeper Life Academy, Maraban Rido, Sakandaren Ecwa da ke Ungwar Maje da Makarantar Bethel Baptist da ke Damishi.

Sauran sun hada da, St. Peters Minor Seminary, Katari, Sakandare ta Prelude da ke Kujama, Sakandaren Ibiso da ke Tashar Iche, Tulip International (Boys) School da Makarantar ‘Yan Mata ta Tulip International.

Har ila yau a cikin jerin makarantun da aka umarci rufewan akwai makarantar sakandaren Goodnews, St. Augustine da ke Kujama, Makarantar CDI da ke Tudun Mare da Kwalejin Adbentist ta Kujama.

Wasikar ta yi gargadin cewa “An shawarce ku da ku yi aiki da abin da wannan wasika ta kunsa yayin da za a dauki matakin hukuncin da ya dace a kan makarantun da aka samu da rashin bin ka’idoji.”

A jiya Litinin ne dai wasu daga cikin iyayen daliban makarantar Cocin Bethel Baptist da ke Kujama a karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna suka bayyana cewa, sama da ‘ya’yansu 100 ne aka sace.

An ruwaito daya daga cikin ma’aikata a makarantar, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, domin ba a bata umarnin yin magana kan lamarin ba, tana bayyana cewa, sama da dalibai 140 ‘yan bindigar suka sace, mata da maza.

Har ya zuwa kammala hada wannan rahoton, mahukuntan makarantar na kan kokarin tattara sunayen daliban da suka bace, domin sanin adadin wadanda aka yi awon gaba da su.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Jalige Mohammed ya fitar ya bayyana cewa, jami’an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da sojin kasa, na sama da kuma ‘yan sanda, bayan samun kiran gaggawa sun afka wa ‘yan bindigar, inda suka samu nasarar kubutar da mutum 26 daga cikin daliban maza da ‘yan mata da kuma wata malama daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: