Sabuwar Mata: Ba Zan Kara Sakin Aure Ba – Adam A. Zango Ya Dauki Alkawari


1 713

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Adam A. Zango, jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ya kammala shiti tsaf domin angonce wa a karo na shida cikin shekara 13.

A katin gayyatar daurin auren ya saka a shafinsa na sada zumunta (Instagram), Zango ya ce zai angonce da wata mai suna Safiya Umar Chalawa, wacce aka fi kira da Suffy, a ranar juma’a mai zuwa da misalin karfe 2:30 na rana.

Za a daura auren ne a masallacin fadar sarkin Gwandu da ke garin Gwandu, a jihar Kebbi.

Da yake nuna dokinsa a kan ssbuwar matar da zai aura, Zango ya ce yana gayyatar kowa da kowa zuwa daurin aurensa.

Sannan ya kara da rubutun cewar zai kasance da sabuwar amaryar har abada. “Zan auri sahiba ta, Safiyya, kuma za ta kasance mata ta har abada Zan zauna tare da ita har abada,” a cewar sa.

Daga baya kuma jarumin ya saka wani faifan bidiyo na sabon gidansa da ake daf da kammala wa.

A faifan bidiyon, ya rubuta, “ina mai gabatar da sabon gida na ga amarya ta. Na kagu na gan ki a cikin gidan nan.”

Majiyar mu ta sanar da mu cewar Zango ya yi aure sau biyar a baya, ya samu ‘ya’ya shida; hudu maza, biyu mata, daga mata biyar da ya aura kafin su rabu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

- Advertisement -

Amina ce matar Zango ta farko da ya aura a shekarar 2006. Ita ce uwar yaron sa na farko, Haidar, wanda yanzu haka ya cika shekara 12 da haihuwa.

Majiyar mu ta legit-hausa ta ce ba ta san abinda ya raba auren Zango da Amina ba. Zango ya kara auren wata matar mai suna A’isha, ‘yar asalin Shika ta karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna.

Ta haifa masa ‘ya’ya maza uku. Jarumin ya auri matar sa ta uku mai suna Maryam daga jihar Nasarawa.

Daga bisani ya auri wata jarumar fim mai suna Maryam AB Yola a Lugbe, Abuja a shekarar 2013. Sun bayyana tare a cikin wani shirin fim din Hausa mai suna ‘Nas’

A shekarar 2015, Zango ya auri Ummul Kulsum daga Ngaoundere a jamhuriyar Kamaru. An yi auren a sirrance.

Ummul Kulsum ce ta fara haifa wa Zango diya mace, wacce ya sanya wa suna Murjanatu.

Safiyya ko kuma Suffy kamar yadda ake kiranta, ita ce za ta kasance matar Zango ta shida da ya aura.

Majiyar mu ta ce Zango ya saki dukkan mata biyar da ya aura a baya, sai dai har yanzu ba ta san dalilin rabuwar sa da matan da ya ke aura ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.