Labarai

Sabuwar Hanyar Karbar Bashi Daga Gwamnatin Tarayya Na Miliyoyin Kudi

Gwamnatin Nijeriya Za Ta Baiwa Masana’antu, Kungiyoyi Masu Raista Da CAC Rancen Milyoyin Kudade, Tun Daga Milyan Guda Har Sama Da Miliyan 500, A Karkashin “Bank Of Industry” Don Farfado Da Masana’antun Nijeriya

Rubutawa✍️✍️✍️
Comr Abba Sani Pantami

A nutsu a karanta da kyau domin a amfana, tare da yiwa al’umma share domin suma su amfana.

Gwamnatin Nigeria za ta bawa masana’antu, Kungiyoyi masu ragista da Hukumar CAC rancen miliyoyin daruruwan kudade, tun daga miliyan guda har sama da miliyan 500, a karkashin “Bank Of Industry” don farfado da masana’antun Nigeria.

Ga manhajar da zaku shiga kuyi ragista anan
👇👇👇
https://apply.boi.ng/register

DAME DAME AKE BUKATA A WAJAN NEMAN RANCEN?

i, Dole sai kana da ragista da Hukumar CAC
ii, Dole sai kana da TIN Number

Matukar baka da ragista da Hukumar CAC, da kuma TIN number, kada kayi APPLY domin aikin banza mutum zai yi.

MENENE “TIN” NUMBER?

“TIN” shine “Tax Identity Number” ana Mallakar TIN number ne ga wa yanda suke da ragista da CAC, zasu je Hukumar dake karbar REVENUE ta kasa mai suna “Federal Inland Revenue Service” “FIRS” ko kuma wadda take karkashin jaha a basu kuma kyauta ne, dole sai kamfani, kungiya suna dashi Kafun su bude account a Banki.

MILIYAN NAWA KOWANNE KAMFANI/KUNGIYA ZASU IYA RANTA?

Kowanne kamfani zai iya neman rancen Miliyoyin Kudade tun daga Miliyan Guda har sama da miliyan 500.

Ga jadawalin kamar haka;
👇👇👇
1, Kasa da Miliyan 5
2, Miliyan 5 zuwa Miliyan 10
3, Miliyan 11 zuwa 20
4, Miliyan 21 zuwa miliyan 50
5, Miliyan 51 zuwa Miliyan 200
6, Miliyan 201 zuwa Miliyan 500
7, Sama da Miliyan 500.

GARGADI:
Ka tabbata ka nemi Wanda ya kware a bangaren harshen turanci, yayi maka APPLY ko kuma kaje shagon CAFÉ, amma ka tabbata ka saka ido da kyau a lokacin da ake cika maka bayananka don kada su cika maka badaidaiba, abun yana da matukar wahala, amma Inshaallah za’a da ce.

YAUSHE KUDIN ZAI SHIGA ACCOUNT DIN MUTUM?

Bayan ka kammala cika dukkannin abubuwan da aka bukata, idan kayi “SUBMIT” zasu turo muku da sako ta gmail dinku, inda zasu tabbatar muku da cewa zasu duba dukkanin bayanan da kuka tura musu nan da zuwa mako Biyu zasu waiwaye ku.

Da zaran sun neme ka tare da yi maka APPROVED Inshaallah kudin zai shiga Account din ku.

Ga manhajar da zaku shiga kuyi ragista anan
👇👇👇
https://apply.boi.ng/register

Karin Bayani Game Da Masu Neman Rancen Bashin Gwamnatin Karkashin Tsarin “Nigeria Youth Investment Fund” NIF
👇👇👇

Tun makon da ya gabata ake ta samun tsaiko wajan “VERIFIED” da kuma shigar da bayanan mutum a manhajar, amma abun yaki saboda yadda al’ummar Nigeria suka yiwa manhajar yawa.

Wasu sun kammala amma wasu har yanzu ko message din “VERIFY” ba’a turo musu ba, matsalar ta shafi Miliyoyin mutane, ba iya kai kadaiba a yi hakuri a daure a cigaba da gwadawa Inshaallah za’a dace.

Rubutawa✍️✍️✍️
Comr Abba Sani Pantami
National Chairman
Arewa Media Writers

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: