Kwanfuta

SABUWAR FASAHAR SARRAFA HOTON BIDIYO TA ZAMANI

 

Akwai sababbin manhajojin sarrafa hotunan Bidiyo na zamani da dama, wadanda sun hada da Manhajar Enlight, KineMaster, Final cut Pro, Cyberlink Power Director 17 ultra, Filmora, Blender, Kenlive, Hitfilm Express, Adobe pro da dai sauransu. Ma su kirkira da fasaha sun samar da wadannan Manhajoji ne domin sauwaka tsarifin hotunan bidiyo daidai da bukatun al’umma da lokaci.

Don karin saukakawa da kawo fasahar bidiyo kurkusa, a yau an samar da wadannan Manhajojin bisa wayoyin hannun wadanda a ke kira android ko smartphone, halin da ya baiwa mutane dama ke kirkirar abubuwa iri-iri don cimma manufarsu kyakkyawa ko akasinta cikin kwarewa da irin fasahar da a da a masana’antar finafinai na Hollywood kadai a ke iya samunta.

Da wannan fasaha kana iya kirkirar dukkan abinda babu shi, ko ka yanko abinda kake so ka dasa shi inda ka so. Ka motsa abinda a zahiri ko dabi’a bashi motsuwa, ko ka sanya harufan zance a bakin wanda yake baya iya maganantuwa. Daga cikin abubuwan da wannan sabuwar manhaja ke iya yi akwai:

1. Kana iya sa abinda bashi da rai motsi, kamar yayi rawa, ko tafiya ko Magana a kuma lokacin da a ka so.

2. Kana iya kara dukkan abinda kake so wani hoton da ka dauka wanda a zahiri babu wannan karin.

3. Kana iya cire muhallin da aka dauki hoton, ka mayar da abinda ka ga dama, misali hoton bidiyon da a ka dauke shi cikin daki ana iya cire wanda aka dauka a mayar da shi cikin daji ko ruwa yadda mai kallo ba zai iya ganewa ba. Kome na iya yiwuwa ta hanyar fasahar chrome key dake cikin wannan manhaja.

4. Kana iya sarrafa hoto ka ba shi kamar da kake so. Ma’ana kana iya canzawa hoto kama daga siffarsa ta hakika da a ka san shi zuwa wani abu dabam.

5. Kana iya sarrafa kala ko siffa, ma’ana abinda yake fari ka mayar da shi baki. Ko bakin mutum ka mayar da shi fari kamar bature ko sabanin haka.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.