Labarai

Sabuwar Dokar da Gwamnatin Jihar katsina ta Gindiya

* Antoshe Hanyar jibiya zuwa Gurbin Baure ga Masu abin Hawa, Amman zasu iyabi ta Funtua.

* Sana Hanyar kankarar zuwa Jibiya itazama zata kasance a rufe saidai abi ta Funtua.

* Sana Manyan Motoci Masu daukar itace adaji Suma an hansu.

* Sana an dakatar da sayar da Dabbobi a kasuwar Jibiya , Batsari, safana, Dan Musa, Kankara , malumfashi, Charanci, Mai aduwa , Kafur, Faskari, Sabuwa, Baure, Dutsinma da Kaita.

* Sana an Hana daukar Shanu da Sauran Dabbobi daga Jihar Katsina zuwa Wata Jihar.

* Sana An hana daukar Mutum 3 kan Babur Sana Masu kananun Motocin daukar passenger kada su Wuce Mutane Ukku.

* Sana an Hana siyar da Babura na Hannu ( Second hand ) a kasuwar Charanci.

* Sana an sake maido da Dokar Hana Hawan abin Hawa daga bakin karfe 10 na dare har zuwa karfe Shidda na Safe .

* An hana sayar da man fetur a cikin jarka a gidajen Mai.

* gidajen Mai Guda biyu ne kadai aka yarje su sayar da Mai fiye dana 5,000 a kananun Hukumomin, Jibiya, Batsari, Safana, danmusa ,Kankara, Faskari, Sabuwa , Dan dume, musawa, Matazu, Dustinma, kurfi, danja da Kuma karamar hukumar kafur.

Wannan Doka bazatayi aiki akan Yan jarida ba, da jami’an Tsaro Hadi da Malaman Lafiya, zasu Iya amfani da ababen Hawansu Kai tsaye.

Wannan dokace da Gwamnan Jihar katsina Rt.hon. Aminu Bello Masari Ya rattabawa Hannu Kuma zata Fara aiki daga Yau 31/08/2021.

– Falalu Lawal, katsina
– 31/08/2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: