Labarai

Sabon Shugaban Kasar Biyafara Ya Bayyana

Wannan Shine Hotan Sabon Shugaban Kasar Biyafara Ya Bayyana

Shugaban Bangaren kungiyar da ke Fafitkar kafa kasar Igbo zalla wato Biyafara, Mista Benjamin Onwuka ya bayyana kafa ‘yantacciyar kasar Biyafara inda ya nada kansa a matsayin Shugaban Kasa. 

 

A cikin sanarwar da ya fitar ya bayyana tsohon Ministan Yada Labarai dan asalin jihar Niger, Farfesa Jerry Gana a matsayin Ministan Sufuri na kasar Biyafara sai Labaran Maku daga Nasarawa a matsayin Ministan Sufurin Jiragen Sama.

Sabon Shugaban Kasan ya kuma nemi hadin kan Tsagrerun Niger Delta wajen bayar da kariya ga sabuwar kasar.