Sabon Mukaddashin CJN Ya Rantsar Da Mambobin Kwamitin Sauraron Kararrakin Zabe 250

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Farawa da iyawa: Sabon mukaddashin CJN ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe 250

Ibrahim Tanko Muhammed, sabon mukaddashin shugaban alkalan Najeriya (CJN) a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe su 250, gidan talbijin din Channels TV ta ruwaito.

Talla

A lokacin bikin kaddamarwar da ya gudana a Abuja a yau Asabar, Muhammed ya bukaci mambobin kwamitin sauraron kararrakin zaben da su gudanar da ayyukansu cikin mutunci da tsoron Allah a zukatansu.

Da farko dai majiyarmu ta rawaito sabbin bayanai da suka bullo kan dalilin da yasa gwamnatin tarayya ba ta jira kotu ta bayar da umurni akan tsige babban alkalin-alkalan Najeriya Walter Onnoghen ba a Abuja a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

An sanya ran cewa Justice Onnoghen zai kaddamar da kwamitocin alkalai 250 da za su jagoranci gudanarwar zabe mai zuwa.

Majiyar tace: “Adadin mambobin da za su zauna a kwamitocin zabe su 250 ne. Kwamitocin sun hada da na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki, kotun sauraron kararrakin zaben gwamna, da kuma na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki na jiha.

“Cire shi da aka yi cikin gaggawa don kokarin dakatar da taron ne ko kuma yunkurin cire sunayen wasu alkalai daga jerin sunayen. Hakan ce za ta kasance.”

Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: