Gwamnatin kasar Amurka a jiya ta kara tabbatar wa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari cewa zasu ci gaba da bayar da dukkanin gudummuwar su wajen yakar ta’addanci da sauran masu tada kayar baya a kasar dai dai iya karfin su.
Wata tawagar yan majalisar tarayyar kasar ne dai da suka samu jagorancin jakadan kasar ta Amurka a Najeriya ne dai suka tabbatar da hakan yayin wata ziyarar aiki da suka kai a kwamandojin kasar da ke bakin daga a barikin sojoji na Maimalari a garin Maiduguri.
A cewa shugaban tawagar ya ce: “Kamar yadda muka saba ba kasar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari taimako, zamu ci gaba ma yanzu tare kuma da doriya ma har sai an kawo karshen dukkan ta’addanci da kuma tayar da kayar baya a kasar.”
Idan mai karatu bai manta ba dai zai iya tuna cewa wasu daga cikin yan shi’a a Najeriya masu fafutukar ganin an sako jagoransu sun rubutawa kasar ta Amurka takarda suna rokon kar a taimakawa shugaba Buhari din.
Add Comment