Labarai

Ruwa da iska mai karfi sun hana bulaguro a Birtaniya

Wani hoton yanayi na BBC na hasashen guguwar Doris
Wasu yankunan na Birtaniya suna cikin shirin ko-ta-kwana na tsammanin ruwa da iska mai karfi da kuma zubar dusar kankara da za a yi a kasar, wadanda za su iya kawo tsaiko a tafiye-tafiye.
An gargadi mazauna yankuna arewacin Ingila da gabashin Anglia da arewacin Wales da kuma Midlands kan su zauna cikin shiri, yayin da yankin Scotland kuwa ke fama da matsanancin zubar dusar kankara.
An soke tashi da suakra jirage da dama a filin jirgin saman Heathrow, an kuma sanar wa da masu zirga-zirga cewa su tsammaci samun tsaiko a kan tituna da tasoshin jiragen kasa.
An yi iska mai karfin gudun mil 87 cikin sa’a daya a gabar tekun Galway a jamhuriyya Ireland, kuma iskar na tunkarar Birtaniya gadan-gadan.
Ana hasashen cewa zubar dusar kankarar zai karu sosai a wasu bangarori na Scotland, yayin da a yammacin Wales kuwa tuni an fara iskar mai tsananin karfi da safiyar Alhamis.

Tsaikon da aka samu

  • Filin jiragen sama na Heathrow ya soke tashin jirage 77 a shafinsa na intanet saboda rashin kyawun yanayi.
  • Filin jirgin sama na Aer Ling ma ya soke tashin dukkan jiragensa zuwa Birtaniya da kuma Ireland
  • Ana samun tsaiko sosai a tasoshin jiragen kasa na Wales da Chiltern da Gabashin Midlands da sauran su, inda jiragen ba sa isa matsaya a kan lokaci
Waves crash over marina wall in BrightonHakkin mallakar hotoPA
Image captionYadda iskar ke ratsa teku
Akwai yiwuwar yanayin ya shafi lalacewar wutar lantarki, inda aka bukaci dk wanda abin ya shafa ya kira wata lamba don neman taimako.
Masu hasashen yanayi sun ce akwai fargabar samun ambaliya mai karfi a Arewacin Ireland, da kuma wadda ba ta kai girman waccar ba arewacin Ingila da kuma Kudancin Scotland.
Sai dai hukumar kula da muhalli ta ce ba ta fitar da wata sanarwar gargadin samun ambaliya ba a Birtaniya.
Ana sa ran ci gaba da samun ruwan sama mai yawa har zuwa karshen makon nan sai dai ba zai kai karfin iskar da ake yi ba wadda ake wa lakabi da Doris.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.