-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Rundunar Yansandan Nigeria Sunyi Amai Sun Lashe


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a Najeriya ta nesanta kanta daga wani rahoto da aka wallafa da ya ce yin jima’i a cikin mota a bainar jama’a ba laifi ba ne.

A cikin wata sanarwa kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas Imohimi Edgal ya ce rundunar ta karyata waccan sanarwar da ke cewa babu laifi idan wasu mutane suka yi jima’i a cikin mota a bainar jama’a.

Sanarwar da babban sufeton ‘yan sanda Chike Oti ya sanya wa hannu ta ce ofishin mai shigar da kara na jihar Legas da lauyoyin rundunar sun tabbatar wa rundunar cewa laifi ne idan wasu suka aikata haka.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Sashe na 134 da Sashe na 136 na dokokin jihar Legas sun fayyace cewa irin wannan abin laifi ne saboda yana karya dokar kasa da ta hana kowa gudanar da wani abu da ya kasance zai iya lalata tarbiyyar al’umma.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

Ya ce duk wanda doka ta samu yana aikata wadannan laifukan zai fuskanci daurin shekara biyu zuwa uku a gidan yari.

Sanarwar ta kuma ce Sashe na 231 na dokokin Tarayyar Najeriya sun bayyana irin wadannan a matsayin laifuka da ka iya sa a daure duk wanda ya aiakta su afadin kasar ban da yankin Arewa mai amfani da tsarin doka na Penal Code..

A saboda haka ne rundunar ta gargadi jama’a da su guji aikata wannan laifin ko da kuwa dukkansu sun amincewa juna.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: