Labarai

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Da Ke Katsina, Ta Kama Ɗan Sanda Da Sojan Bogi Da Ke Tare Mutane A Hanya

Daga Zaharaddeen Gandu

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke wasu ‘yan fashi da makami guda biyu da suke yin sintiri a matsayin jami’an rundunar sojojin Najeriya da na ‘yan sandan ƙasar, domin yi wa jama’ar da ba su ji ba su gani ba fashin kayayyaki masu daraja, kamar yadda Daily Post ta rawaito.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da:

 

Yahaya Armaya’u mai shekaru 35 (wanda aka fi sani da KOFUR) da Bashir Isiyaku mai shekaru 32 (wanda aka fi sani da SOJA) daga ƙauyen ‘Yar-Kaware, cikin ƙaramar hukumar Ƙafur ta jihar Katsina, an gurfanar da su a gaban manema labarai a ranar Juma’ar da ta gabata a rundunar ‘yan sandan jihar.

Waɗanda ake zargin sanye da kayan ‘yan sanda da na sojoji ne, suna cikin motar Golf, sun je ƙauyen Mahangi ne, inda suka kai hari ga wani mai suna Zaharadin Ya’u da ke ƙauyen Sheƙa a ƙaramar hukumar Ƙafur ta jihar a matsayin jami’an soji da na ‘yan sanda.

Waɗanda ake zargin sun tsoratar da shi da mari, inda a ƙarshe suka yi masa fashin babur mai suna Boxer, wanda adadin kuɗin mashin ɗin zai kai kimanin naira dubu ɗari biyu (N200,000).

Hakazalika, ta hanyar amfani da wannan dabara, waɗanda ake zargin sun kai hari tare da yi wa wani mutum mai suna Usman Sani ɗan ƙauyen Yari-Bori fashi babur ɗinsa.

A yayin gudanar da bincike, waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun yi amfani da irin wannan hanya, tare da yin fashin baburan dambe guda huɗu (4) a wurare daban-daban tsakanin Malumfashi da babban birnin tarayya Abuja.

‘Yan sandan sun ƙwato abubuwa masu zuwa daga waɗanda ake zargin: sarƙa, hular fuskar ‘yan sanda, T-shirt Camouflage na sojoji, da sauransu.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.