Cin Hanci da Rashawa

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wani korarren kurtun dan sanda cikin yan fashi da makami

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wani korarren kurtun dan sanda cikin yan fashi da makami

 

Rundunar yan sandan Nijeriya ta Bauchi ta bayyana nasarar cafke wani korarren kurtun dan sanda mai suna Muhammed Jawat, mai shekaru 27 tare da wasu mutum biyu da suka hada da Muhammed Ahmed dan shekaru 27 gami da Husaini Ahmad mai shekaru 19 da laifin aikata fashi da makami.

 

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ahmed Muhammed Wakili shi ne ya bayyana hakan a shafinsa na facebook a ranar Litinin,

 

Ya ce bayan rundunar yan sandan ta sami labarin sirri game da yan fashin, ta kai masu samame a tashar mota ta garin Jama’are inda ta yi nasarar damko su

 

Yan sanda sun kuma sami yan fashin da wata karamar bindigar hannu kirar gida, da kuma kwalson alburusai da babu komai a ciki.

 

Kakakin rundunar ya bayyanawa Zuntu online news cewa wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata laifin da ake zarginsu da shi na aikata fashi da makami, inda ya ce bayan kammala binciken yan sanda, za su tasa keyarsu zuwa gaban kuliya manta sabo