RUNDINAR ‘YAN SANDA SUNYI BABBAN KAMU
Daga Datti Assalifya
Rundinar kwararrun ‘yan sanda na IGP Intelligence Response Team (IRT) karkashin jagorancin DCP Abba Kyari sun samu nasaran cafke wasu mutane hudu da suke sana’ar harhada magunguna na bogi a jihar Lagos
Bayan bayanan sirri da aka samu a kansu, jami’an ‘yan sanda sunbi diddiginsu aka cafkesu tare da gano dakin da suke harhada magungunan, kamar yadda za’a gani a wannan hoton
Baba shakka wadannan mutane azzalumai sun cancanci hukuncin kisa, domin Allah ne kadai Ya san adadin mutane ‘yan Nigeria da suka hallaka a dalilin shan kwayoyi na bogi da suka hada
Don Allah jama’a ku kalli dakin hada maganin da kyau, cutar da take a cikin wannan kazamin daki ita kanta matsalace babba, sannan ga maganin na bogi ne suke bugawa
Shiyasa ‘yan Nigeria musamman talakawa suna ta shan magunguna amma maimakon su samu lafiya sai ma cutar ta karu, sai anyi dace da kyar ake samun sahihin magani ko kuma mutum ya sayi maganin kasar waje mai tsada
Hakika DCP Abba Kyari da rundinarshi sunyi aikin jihadi na ceton rayuka Allah Ka saka musu da alheri.
Kwanaki akwai wani bawan Allah da naga yana cewa ya san wani mugun inyamuri da yake safarar maganin bogi daga Enugu zuwa Adamawa yana bada cin hanci mai tsoka wa jami’ai kafin ya wuce da maganin
Duk wanda ya karanta wannan sakon sannan yana da masaniya a kan inda ake hada magani na bogi, ko kuma ya san wadanda suke safarar maganin bogi ya min ni Datti Assalafiy magana ta inbox don Allah.
Muna rokon Allah duk wani mugu da yake samar da kwayoyin bogi a ko’ina yake a Nigeria Allah Ka fallasa asirinsa Amin