Labarai

Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Bayyana Sabon Shirin Yaki Da Ta’addanci

Daga Sulaiman Ibrahim,
Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, a yau zai kaddamar da sabbin atisayen tsaro guda uku a duk fadin kasar.

Kakakin rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya kira atisayen “Golden Dawn ”,” Enduring Peace ” da “Still Water ”.

Ya ce, an yi hakan ne don a kula da duk wani nau’in kalubalen rashin tsaro da kuma ba da damar walwalar zirga-zirgar mutane yayin da bikin Kirsimeti ke gabatowa na karshen shekara.

Ya ce Babban Hafsan (COAS) shi zai kaddamar da dukkan atisayen a yau a Ovie-Emene, karamar hukumar Enugu ta Gabas ta Jihar Enugu, wurin taron “Exercise Golden Dawn’ ’.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: