Rahoto daga kafafen yada labarai na Radio France International ya labarta cewa Rundunar sojin Najeriya ta ce ba zata cigaba da lamuntar yi mata kazafin cewa tana cin zarafin dan adam ba, daga kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra wadda aka fi sani da IPOB.
Rundunar sojin ta maida martani ne kan sanarwar da kungiyar ta IPOB ta fitar cewa sojin Najeriya sun harbe wasu ‘yan kungiyar 11 a ranar 20 ga watan janairun da ya gabata, yayinda suke gudanar da zanga zangar nuna goyon bayansu ga nasarar da Donald Trump ya samu na zama shugaban Amurka.
Add Comment