Rundunar Sojin Nijeriya ta shirya taron bajen kolin kayayyakin yaki na kwanaki uku a Abuja, inda ta gabatar da motoci da bindigogin kai farmaki daban-daban.
A ranar litinin ga watan Fabrairu aka fara gabatar da wani taro a Babban Dakin Taro na “Nigerian Army Resource Centre” dake barikin Mambilla a Abuja, inda Rundunar Sojin Nijeriya ta shirya baje kolin kayayakin yaki da gabatar da motoci da bindigogin kai farmaki na daban-daban.
Babban Hafsan Sojin Nijeriya Janar “Tukur Buratai ya jagoranci wannan taron, tare da halartar Ministan Tsaro Janar Dan Ali, da Ministan Kimiyya da Fasaha Dr Ogbonnaya Onu.
Ministan Tsaron, wanda ya jagoranci manyan baki a yayin zagayen kaddamar da kayayakin yakin ya bayyana cewa “Wannan yunkuri shine irinsa na farko da Nijeriya ta fara kera kayayakin yaki na kanta, kuma hakika wannan babban nasara ce da Nijeriya ta cimma a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shima Babban Hafsan Sojin, Tukur Buratai ya ci gaba da cewa wannan duka yana daga cikin yunkurin kawo karshen ta’addanci a Nijeriya,
“Muna tabbatar wa al-ummar Nijeriya da cewa kowa ya kwantar da hankalinsa da yarda Allah zamu samu zaman lafiya a kasa, zamu kawo karshen kowane ta’addanci kamar yadda ake gani mun riga mun gama da Boko Haram illa kawai kananan hare-haren da ake samu nan da can”
Babban Bako mai jawabi, Farfesa Buba Bindir, Tsohon Darakta Janar na Kimiyya da Fasaha kuma Sakataren Gwamnatin jihar Adamawa ya bayyana irin muhimmancin da ke tattare da kimiyya da Fasaha wanda ya kai da nasarar samar da wadannan dabaru,
“Babu wata kasa a duniya da ta taka tsanin cigaba a duniya face sai da ta samu nasara a fannin kimiyya da fasaha, don haka mu ma a Nijeriya mun kama hanyar wannan nasara muddin muka cigaba da dogaro da kanmu”
Add Comment