Rundunar Sojin Najeriya Tayi Kyakkyawan Shirin Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Zabe

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rundinar sojin Nigeria ta gabatar da wani tsari na musamman ta hanyar yin amfani da manyan na’urori mai kwakwalwa (Computers) masu amfani da tauraron ‘dan-adam (Satellite) wanda za’a iya ganin dukkan abinda yake faruwa a fadin tarayyar Nigeria a lokacin zabe ta gilashin na’urorin kuma a lokaci guda (Situations Room)

Haka zai iya faruwa idan aka tura jiragen leken asiri marassa matuki (drone) a kowace jiha, wannan zai bada dama a cikin daki guda a kalli dukkan abinda yake faruwa a Nigeria da dukkan zirga-zirgan da mutane keyi kuma a lokaci guda

Talla

Manufar da ya sa rundinar sojin Nigeria tayi wannan tsarin shine don a inganta tsaro tare da kai agajin gaggawa a inda na’ura ta leko wata barazana na tsaro a lokacin zabe, ta hanyar tura jiragen yaki masu saukar ungulu ko kuma yin amfani da sojojin kundunbala ta Kasa idan bukatar hakan ya kama

An gabatar da wannan sabon tsarin a cibiyar yaki da ayyukan ta’addanci da miyagun laifuka da ake aikatawa a kafar yanar gizo na rundinar sojin Nigeria dake birnin Tarayya Abuja, wato “Nigerian Army Headquarter’s Cyber Warfare Command”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Wanda ya jagoranci bude wannan sabon tsarin shine shugaban rundunonin sojin Nigeria gaba daya Chief of Defence Staff (CDS) Janar Olanisakin tare da rakiyar shugaban sojojin ‘kasa Chief of Army Staff (COAS) Laftanar Janar Buratai

Wannan matakin yayi, muna kira ga al’umma da cewa kowa ya shiga taitayinsa a lokacin zabe, a gujewa duk wani mataki da zaiyi sanadin tayar da hankali, a bi doka a zauna lafiya, domin hukumomin tsaro sunyi kyakkyawan shiri irin wanda ba’a taba yinsa ba a tarihin zabe a Nigeria

Muna rokon Allah Ya sa ayi zabe lafiya a kammala cikin nasara ba tare da tashin hankali ba.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: