Labarai

Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi wani Gwamna

– Rundunar Sojin Najeriya ta ja kunnen Gwamna Fayose

– Rundunar ta fadawa Gwamnan ya daina abin da yake yi

-Ta kara da cewa an ga canji a wajen Sojin kasar yanzu

Mun samu labari cewa Rundunar Sojin kasar nan ta ja kunnen Gwamna Ayodele Fayose na Jihar Ekiti kan irin abubuwan da yake yi mata.

 

Mun fahimci cewa Rundunar Sojin ta fadawa Gwamnan na Jihar Ekiti ya daina abin da yake yi na surutai marasa kan gado game da Sojojin kasar da ke bakin daga. Rundunar Sojin kasar ta ce yanzu fa ba kamar da ba ne don haka Gwamnan ya rufe bakin sa.

Rundunar Sojin ta bayyana wannan ne a wani jawabi da ta fitar game a shafin ta na Tuwita. Ta kara da cewa yanzu Sojin kasar ba kamar da ba lokacin da ake zargin Sojoji da rashin gaskiya wajen yaki da Boko Haram. Kwanan nan Gwamnan na Jihar Ekiti Ayo Fayose ya kara jaddada cewa shi zai karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2019.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.