-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Rundunar Sojin Najeriya Ta Fatattaki Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Daga Borno


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da dakatar da duk wasu ayyukan jin kai da wata hukumar majalisar dinkin duniya dake kula da kanan yara, UNICEF takeyi a jahar Borno, dama sauran yankunan Arewa maso gabas gaba daya.

Jaridar PR Nigeria ta ruwaito mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar Sojin Najeriya, Kanal Onyeama Nwachukwu ne ya sanar da haka a ranar Juma’a 14 ga watan Disamba, inda yace sun dauki wannan mataki ne duba da yadda UNICEF ta ke yi ma yaki da yan ta’adda zagon kasa.

Sojoji sun zargin UNICEF da kokarin cin dunduniyarsu a yakin da suke yi da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, inda suka ce UNICEF da wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake rajin tallafa ma yan gudun hijira suna horas da matasa akan dabarun yaki.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wadannan ayyukan kungiyoyi da ma wasu na daban yasa rundunar ta daukesu a matsayin abokan gaba dake kokarin mayar da hannun agogo baya, sa’annan ta bayyana ayyukansu a matsayin raninin hakulan yan Najeriya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 656

- Advertisement -

“Da wannan ne muke sanar da dakatar da ayyukan UNICEF a yankin Arewa maso gabas tunda dai sun yi watsi da aikin dake gabansu na kulawa da kananan yara marasa galihu dake gudun hijira a sansanoni daban daban a fadin yankin, sun fara shirya wasu kulle kulle.

“A yanzu UNICEF tana yi ma yaki da ta’addanci zagon kasa ta hanyar yada jita jitan cin zarafin daga bangaren Sojoji, haka zalika suna horas da yan ta’adda akan dabarun yaki, kuma suna biyan masu yi ma kungiyar Boko Haram leken asiri.

“Mun samu labarin UNICEF ta horas da yan ta’addan ne daga ranar 12 ga watan Disamba na 2018 zuwa 13 ga watan Disamba a dakin taro na ma’aikatan kudi na jahar Borno dake garin Maiduguri, kuma ba zamu lamunci hakan ba.” Inji sanarwar.

Sai dai wasu masana doka suna ganin ba lallai bane wannan hukunci na rundunar Soji yayi tasiri saboda a cewarsu Sojojin basu da ikon daukan wannan hukunci, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kadai zai iya zartar da wannan hukunci, amma zuwa yanzu babu tabbacin shi ya bada umarnin ko a’a.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: