Labarai

Rufe Boda Da Muka Yi Bai Amfane Mu Da Komai Ba, Cewar Shugaba Buhari

Daga Comr Abba Sani Pantami

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da cewa, duk da kokarin da gwamnatinsa tayi na rufe boda a kasar nan hakan bai hana shigo da makamai cikin kasar nan ba bisa ka’ida ba.

Sai dai shugaban ya siffanta faruwar hakan da yanayin da kasar Libya take ciki, ya ce matukar Libya zata cigaba da kasancewa a halin da take ciki, to lallai haramtattun makamai da harsasai da sauran su zasu cigaba da kwarara yankin Sahel.

A bayanin mai bashi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, yace Shugaban ya yi jawabi ne lokacin da ya karɓi bakuncin wakilan UN, shugaban UN da sakataren sa na Africa, lokacin da sukazo yin bankwana a fadar shugaban kasa, Villa, dake Abuja.

Bayanin shugaban da akayi wa take da ‘Rikicin Libya ne babbar matsalar kasasheb yankin Sahara, inji shugaba Buhari.’

Idan zaku iya tunawa, Najeriya ta kulle bodar ta a watan Augustan shekarar 2019 da zummar dakile fasa kwauri a ƙasar.

Sai dai, an bube bodar a watan Disamba 2020 saboda aiwatar da yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen Africa wadda ta fara aiki 1 ga watan Janairu, 2021.

“Mun rufe bodar mu ta ƙasa na tsayon shekara ɗaya, amma makamai d sauran makamantansu sun cigaba da kwarara cikin ƙasar ba bisa ka’ida ba. Matukar Libya zata cigaba da kasan cewa cikin rikici to matsalolin mu ba zasu kare ba.”

“Ya kamata mu jure waɗan nan matsalolin, amma da sannu za muga bayan su gaba ɗaya,” a cewarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: